Gudunmawar Marubuta Mata Hausa ga Adabin Nijeriya: Bincike a Jihar Katsina

📖 ABSTRACT/OVERVIEW

Wannan bincike ya yi nazari kan gudunmawar marubuta mata Hausa ga adabin Hausa da kuma adabin Nijeriya baki ɗaya, musamman daga shekarun dubu biyu zuwa yanzu a Jihar Katsina. Tun da maza su ne suka fi rubuta adabin Hausa a zamanin da ya gabata, yanzu mata suna ɗaukar matsayi a fagen rubutun Hausa. Binciken ya yi amfani da hanyar tattaunawa da marubuta mata a Jihar Katsina da kuma nazarin littattafan da suka rubuta. An tattara bayanai game da rayuwarsu da dalilan da suka sa suka fara rubuta da kuma irin ƙalubalen da suke fuskanta a fagen rubuta. Sakamakon ya nuna cewa marubutan mata Hausa a Katsina suna ƙara rubuta littattafai kan batutuwan da suka shafi rayuwar mata, kamar zaman aure da ilimi da 'yancin mata. Binciken ya gano cewa ko da yake sun sami nasara, amma har yanzu suna fuskantaw gane matsaloli kamar karancin bayar da tallafi da rashin damar bugawa. Wannan bincike yana nuna muhimmancin haɓaka damarmaki ga marubuta mata Hausa a Nijeriya. Kalmomin bincike: mata marubuta, adabin Hausa, rubuta, Katsina, tattalin arziki.

Need Complete Chapters of the Above Topic?

Get high-quality, Zero-AI research materials with current citations.

Request via WhatsApp 💬
Departments# Hausa